Saturday, January 11
Shadow

Karanta Jihohin da suka fi biyan masu Gàŕķùwà da mutane kudin fansa da yawa

Jihohin Kudu maso gabas, watau jihohin Inyamurai ne suka fi biyan masu garkuwa da mutane kudi da yawa dan karbo ‘yan iwansu da aka yi garkuwa dasu.

A gaba daya Najeriya, an biya masu garkuwa da mutane jimullar Naira Biliyan 1.048 a matsayin kudin fansa inda jihohin kudu maso gabas na inyamurai suka biya jimullar Naira Miliyan dari hudu da sha tara 419.2 Million.

Wannan shine kaso 40 na jimullar kudij fansar da aka biya a Najeriya.

A jihar Anambra ne aka fi biyan kudin fansar inda aka biya masu garkuwa da mutane jimullar Naira miliyan 350.2 a jihar.

Mutanen jihar Imo sun biya masu garkuwa da mutanen Naira Miliyan 39.

Karanta Wannan  Hotuna: Jirgin kasa daga Kaduna zuwa Abuja yayi Hadari

Sai jihar Abia data biya Jimullar Naira Miliyan 25 ga masu garkuwa da mutanen, mutanen jihar Enugu sun biya Naira Miliyan 4 ne ga masu garkuwa da mutanen dan karbo danginsu da aka sace inda jihar Ebonyi ta biya Naira miliyan 1.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *