Ga Sunayen Matayen Manzon Allah(Sallallahu Alaihi Wasallam) kamar haka:
Khadijah Bint Khuwaylid.
Sawdah Bint Zam’ah ibn Qays.
A’ishah Bint Abi Bakr al-siddiq.
Hafsah Bint Umar.
Zaynab Bint Jahsh.
Umm Habibah bint Abi Sufyan.
Maymunah Bint Al-Harith.
Safiyyah Bint Huyayy ibn Akhtab.
Allah ya kara yadda dasu.
Khadijah itace matar Annabi(Sallallahu Alaihi Wasallam) ta farko wadda ya aura yana da shekaru 25 a Duniya kuma bai kara auren wata ba har sai da ta rasu. Itace ta haifi duka ‘ya’yan Annabi(SAW) in banda Ibrahim.
Bukhari ya ruwaito daga A’isha tana cewa, duk cikin matan manzon Allah(SAW) ta fi yin kishi da Khadijah duk da bata zauna da ita ba, dalili kuwa shine yanda manzon Allah (SAW) yake yawan ambatonta.