Tuesday, January 14
Shadow

An gano wata hanyar da ‘yan ìndìgà ke amfani da ita dan samun màyàkà da yawa ta hanyar amfani da mata

Shugaban rundunar sojojin Najariya, CDS, Christopher Musa ya bayyana cewa a yanzu ‘yan Bindiga da yake babu wani gari dake hannunsu sun fito da dabarar samun mayaka.

Yace a baya sukan kai hari garine su samu maza majiya karfi ko kana so ko baka so a tursasa maka ka dauki makami ka shiga cikinsu, idan ka kiya su yankaka.

Yace amma yanzu basu da wannan damar.

Ya bayyana hakane a hirar da aka yi dashi a gidan talabijin na Arise TV.

Ya kara cewa, yanzu dabarar da ‘yan Bindigar suke yi shine sukan samu mata su yi ta dirka musu ciki akai-akai suna haihuwa dan su yi amfani da yaran a matsayin mayaka.

Karanta Wannan  Hotuna: An kamasu suna yiwa karuwai Fashi da makami

Yace idan sukawa mace ciki ta haihu, bayan wata 4 zasu sake saduwa da ita dan ta kara daukar wani cikin.

Yace a kwanannan wasu ‘yan Bindiga da suka mika wuya suka ajiye makamai su dubu dari da ashirin, guda dubu sittin duk kananan yara ne.

Yace irin wadannan yara sai sun fi ‘yan Bindigar da ake dasu a yanzu illa saboda sun tashi sun ga kisa ba komai bane.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *