Wani mutum dake bin addinin gargajiya a jihar Oyo ya kona Qur’ani inda lamarin ya so tayar da rikicin addini a jihar.
Lamarin ya farane bayan da wasu malaman addinin Musulmi jihar suka bayyana aniyarsu ta kafa kotun shari’ar musukunci a jihar.
Maganar ta tayar da kura wadda ta kai ga har sai da DSS suka gayyaci malaman suka sanar dasu cewa basu da hurumin yin hakan, kundin tsarin mulkine kadai ke da hurumin kafa kotu a Najeriya amma ba wani mutum ko wata kungiya ba
Malam sun hakura inda suka buga a jarida cewa sun fasa kafa kotun shari’ar musuluncin a jihar ta Oyo.
Bayannan ne sai kuma aka samu wani mabiyin addinin gargajiya ya fito ya kona Qur’ani ya dauki bidiyo ya wallafa a kafafen sada zumunta inda yace kuma babu abinda za’a masa kan wannan aika-aika da yayi.
Tuni dai hukumar tsaron farin kaya ta DSS ta kama mutumin kuma tace zata gurfanar dashi a gaban kotu dan hukuntashi.