Friday, February 7
Shadow

Gwamnatin tarayya ta kara yawan kudin ciyar da masu laifi a gidan yari inda a yanzu kowanne mutum daya za’a rika ciyar dashi akan Naira 1,125 a kowace rana

Gwamnatin tarayya ta kara yawan kudin ciyar da masu laifi a gidan gyara hali wanda aka fi sani da gidan yari a kasarnan daga Naita 750 zuwa Naira 1,125 a kullun

A baya dai da ake ciyar da ‘yan gidan yarin akan Naira 750 a kullun, ana cire kudin haraji da sauransu wanda a karshe Naira 500 ce take raguwa a matsayin abinda za’a ciyar da ‘yan gidan yarin sau uku a rana.

Shugaban gidajen gyara hali na Najeriya, Sylvester Ndidi Nwakuche ne ya bayyana haka a wani taro da yayi da jami’an hukumar kula da gidan gyara halin.

Ya sha Alwashin ci gaba da neman inganta rayuwar masu laifi da ake tsare dasu.

Karanta Wannan  Kalli Hoto: Yanda wani mutum ya Kàshè kansa a Abuja

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *