Wednesday, January 15
Shadow

Pep Guardiola ya saki matarsa bayan shekaru 30 su na tare

Kocin Manchester City, Pep Guardiola, da matarsa, Cristina Serra, sun rabu bayan shekara 30 tare.

Daily Trust ta ce, a cewar rahotanni daga Spain, rabuwar ta kasance “cikin lumana da fahimtar juna.”

An ce sun yanke shawarar kawo karshen auren nasu ne tun a watan Disamba, sai dai iya makusantansu ne su ka san labarin rabuwar.

An gargadi abokai da dangi kada su bayyana labarin sakin.

A 2019, Serra ta bar birnin Manchester tare da ɗaya daga cikin ƴaƴansu domin komawa Barcelona don kula da kasuwancin kayan kwalliyarta.

Daga baya, ta ci gaba da raba lokacinta tsakanin birnin Spain da London, yayin da suke ci gaba da mu’ammala, amma Guardiola ya ci gaba da zama a birnin Manchester.

Karanta Wannan  Shugaba Tinubu zai halarci taron ci gaban Kasashe a Abu Dhabi

Guardiola da Serra sun hadu a shekarar 1994, lokacin da ya ke da shekara 23 ita kuma ta na da shekara 20, amma ba su yi aure ba sai a 2014.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *