Babban bankin Najeriya, CBN ya ci tarar bankuna da yawa saboda kin sakawa kwastomominsu kudi a ATM su cire musamman lokacin bukukuwan karshen shekara.
Bankin yace ya dauki wannan mataki ne dan nuna rashin amincewa da kin rabawa mutane kudi da bankunan ke yi.
CBN yaci kowane bankin tarar Naira Miliyan 150.
Hakan ya biyo bayan gargadin da bankin yawa bankunan na su wadata mutane da kudi amma suka ki yi, CBN ya aika wakilai zuwa wadannan bankunan kamin daukar matakin tarar.
Bankunan da aka ci tarar sune, Fidelity Bank Plc, First Bank Plc, Keystone Bank Plc, Union Bank Plc, Globus Bank Plc, Providus Bank Plc, Zenith Bank Plc, United Bank for Africa Plc, da Sterling Bank Plc.