Sunday, February 8
Shadow

Da Duminsa: An bukaci a saka Rev. Ezekiel Dachomo a Addu’a, Ciwon Hantane ya kamashi shiyasa aka ji shi shiru ya daina magana akan Mhuzghunawar da akewa Kiristoci a Najeriya

Rahotanni daga jihar Filato sun bayyana cewa shahararren Faston nan me magana akan zargin Mhuzghunawa Kiristoci a Najeriya, watau Rev. Ezekiel Dachomo ya kamu da cutar Hanta

Wani dan jarida daga jihar me suna, Masara Kim Usman ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ta shafinsa na sada zumunta.

Yace Kiristoci su saka Rev. Ezekiel Dachomo a Addu’ar Allah ya bashi lafiya.

Dama dai a baya ya taba kamuwa da cutar inda matarsa ta bashi kyautar daya aka dasa masa, saidai yanzu ciwon ya sake dawowa.

Karanta Wannan  Kalli Bidiyon abinda Iwobi yayi da ya dauki hankula wanda ya nuna cewa Rafali yana goyon bayan Morocco

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *