Friday, January 17
Shadow

Ana zargin shugaban bankin First Bank da satar Naira Biliyan 12.3

Rahotanni sun bayyana cewa hukumar yaki a rashawa da cin hanci, EFCC zata gurfanar da tsohon shugaban bankin First Bank Stephen Onasanya a gaban kotu bisa zargin satar Naira Biliyan 12.3.

Babbar kotun tarayya dake Legas ta saka ranar 20 ga watan Janairu dan fara sauraren karar da EFCC ke yi akan Onasanya da shugaban kamfanin Flourmills Group, Oba Otudeko.

Akwai kuma Soji Akintayo wanda shima yana cikin wadanda ake zargi da kuma wani kamfani me suna Anchorage Leisure wanda duka ake zargin sun hada hannu wajan yin wannan sata.

 Ana zargin sun aikata satarne a tsakanin shekarun 2013 zuwa 2014.

Karanta Wannan  An kama matashi dan shekaru 19 da ya kàshè dansa me kwana 3 a jihar Adamawa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *