Friday, January 17
Shadow

Ciwon suga da magani

Ciwon sugar yana kama mutum ne idan suga ko abinda ake cewa Glucose a turance yayi yawa a jikin mutum. Kuma ciwone dake kama kowane irin mutum ma’ana babba da yaro na iya kamuwa da cutar.

Hakanan ciwon suga a mafi yawan lokuta yana da tsanani, watau zai iya kasancewa tare da mutum har iya tsawon rayuwarsa. Saidai ana iya kula dashi da maganceshi.

A wannan rubutu zamu yi bayani akan ciwon suga da duk wani abu da ya shafeshi hadi da magani sadidan wanda da yardar Allah ana warkewa. Idan ana bukatar maganin ana iya kiran wannan lamba, 09070701569, muna aikawa kowace jiha a fadin Najeriya.

Meke kawo ciwon suga

Kamar yanda muka yi bayani a baya, yawan suga a jinin mutum, watau Glucose a turancene ke kawo ciwon suga. Mafi yawanci wadanda basa motsa jiki, da masu fama da yawan kiba, da wanda basa cin abinci me gina jiki sun fi fama da ciwon suga.

Hakanan ana gadon ciwon suga.

Hakanan mace me ciki a yayin laulayin cikin zata iya yin fama da ciwon suga.

Masu yawan cin abincin gwangwani dana leda dana kwali, watau irin madarar gwagwani, lemun kwalba, Yegot, Chakulan, Biskit da sauransu na cikin hadarin kamuwa da cutar sugar.

Karanta Wannan  Me ke janyo ciwon baya: Maganin ciwon baya mai tsanani

Masu yawan shan taba ma na cikin hadarin kamuwa da ciwon sugar.

Menene alamomin ciwon sugar

A mafi yawancin lokuta, ciwon suga yakan zo babu wata alama, amma mafi yawan alamun da ake gani tattare da me ciwon suga sun hada da, yawan kishiruwa ko yawan fitsari, yawan gajiya, rama, da raguwar karfin ido, watau mutum ya daina gani da kyau.

Idan ciwon suga yayi tsanani, mutum zai rika jin matsananciyar yunwa sannan idan yaji ciwo zai rika dadewa bai warkeba.

Ciwon suga na kuma sa yawan bacci, ciwon kai, da bugawar zuciya da sauri.

Maganin ciwon sugar

A addinance, kowace cuta tana da magani, kuma kamar yanda muka bayyana a sama, muna da maganin ciwon suga sadidan wanda da yardar Allah ana warkewa, ga me bukata sai ya mana magana ta wannan lambar a WhatsApp ko ya kira: 09070701569

Ciwon Suga a likitance bashi da magani, a cewar masana, tunda sugar ne yayi yawa a jinin mutum wanda ake cewa Glucose, to babbar hanyar maganin suga shine sai a daidaitashi daidai yanda jiki ke bukata.

Karanta Wannan  Amfanin alum a gaban mace

Likita kwararre daga jami’ar University of California San Francisco (UCSF) School of Medicine dake kasar Amurka, Dr. Obidiugwu (Kenrik) Duru wanda kuma ke bincike akan ciwon suga yace babbar hanyar daidaita suga a jikin mutum shine a rage cin abinci.

Akwai hanyoyi da yawa na rage cin abinci kamar yanda ya bayar da shawara, yace ana iya amfani da maganin rage kiba, musamman ga masu matsananciyar kiba, sannan ana yin tiyata wadda ke cire kitse daga cikin mutum kuma ta tsuke cikin ta yanda za’a rika cin abinci kadan.

To a addinance, zamu iya cewa, me ciwon sugar idan zai iya dagewa da yin azumi zai iya samun sauki kenan.

Abincin mai ciwon sugar

Masana kiwon lafiya sunce abincin da ya kamata me ciwon sugar ya rika ci sun hada da Kifi, Nama, ganyayyaki irin su latas, Kabeji, Zogale da sauransu.

Hakanan ana son cin kayan itace irin su Apple, Gwaba, Yalo da sauransu.

Ana kuma son cin Abinci masu dussa irin su masara, gero, shinkafa ‘yar gida, wake da sauransu.

Karanta Wannan  Maganin Kaikayin gaban mace

illolin ciwon suga

Illolin ciwon suga na da yawa, ga wasu daga ciki kamar haka:

Yana taba lafiyar zuciya: Ciwon suga na iya kawo bugun zuciya, ciwon hawan jini, da kuma lalacewar zuciyar gaba daya.

Yana taba lafiyar Idanu: Ciwon sugar na taba lafiyar idanu inda yakan iya sa mutum ya makance.

Yana taba lafiyar Kwakwalwa: Ciwon sugar na lalata jinin dake gudana a kwakwalwar mutum inda hakan kan kai ga kamuwa da cutar mantuwa ko kuma cutar shanyewar barin rabin jiki.

Yana taba lafiyar Kafa: Ciwon sugar na iya lalata jijiyoyin kafar mutum wanda zai iya kaiwa ga kamuwa da cutar daji da zata iya kaiwa ga yanke kafar.

Ciwon sugar na taba lafiyar ciki: Yana iya lalatawa mutum ciki ta yanda abinci ba zai rika narkewa ba yanda ya kamata.

Yana taba lafiyar Jima’i: Ciwon sugar na taba lafiyar jima’i ta yanda yake lalata jijiyoyi da rage gudanar jini yanda ya kamata wanda hakan ke hana mazakutar namiji mikewa da kyau sannan yake sa gaban mace bushewa.

maganin ciwon suga na gargajiya

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *