Shugabar Jam’iyyar ‘yan ra’ayin mazan jiya ta kasar Ingila, UK Conservative Party, Kemi Badenoch ta sake sukar ‘yan Najeriya duk da cewa ita ‘yar asalin Najeriyar ce.
Da take magana ta farko a shekarar 2025 a wajan wani taro na musamman ranar Alhamis, Kemi tace bata son ingila ta zama kamar Najeriya, tace ta ga yanda danginta masu hali suka tsiyace saboda rashin gwamnati me kyau da tsadar rayuwa da ta yi yawa.
Kemi na ‘yar shekaru 16 ta bar Najeriya zuwa kasar Ingila da kudin babanta na karshe wanda basu wuce fan £100 ba.
Kemi ta kara da cewa, tana aiki tukuru domin ganin wahalar da ke Najeriya bata maimaitu a kasar Ingila ba.
A baya, Kemi ta zagi ‘yan Najeriya da cewa ‘yan fashi da makami ne.