Wasu rade-radi sun bayyana a kafafen sada zumunta cewa gwamnatin tarayya ta bukaci tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya je wata kotu a kasar Faransa yayi bayani.
An shigar da wata karane kan aikin tashar wutar lantarki ta Mambila inda ake neman Dala Biliyan $6.
Saidai a martanin da me magana da yawun shugaban kasa, Bayo Onanuna ya fitar yace wannan magana ba haka take ba.
Ya tabbatar da cewa, an shigar da kara wanda ake yinsa a sirri kuma duka manyan mutanen da suka je suka yi bayani a wajan kotun, sun yi hakanne bisa radin kansu da kuma nuna kishin kasa amma ba gwamnatin tarayya ce ta tursasasu ba.
Ya kara da cewa, ko kadan bai kamata ace an wallafa labarin shari’ar ba saboda ta sirri ce har sai kotu ta kammala bincikenta.
Saidai yace gwamnatin na godiya ga duka wadanda suka je suka bayar da shaida akan lamarin bisa kishin kasa da suka nuna.