Wata matar aure wadda ‘yarsanda ce ta jawo cece-kuce bayan da ta baiwa Saurayi lambar wayarta.
Matar wadda sunanta Chioma an ganta a cikin wani faifan bidiyon dake ta jawo a kafafen sada zumunta inda Saurayin ya kirata gefen titi.
Ya tambayeta, tana da aure ta amsa mai cewa Eh tana da aure inda yace yana sonta sannan ya karbi lambarta.
Da yawa dai sun yi Allah wadai da wanda ya dauketa bidiyon sannan wasu sun yi Allah wadai da saurayin da be kyaleta ba tunda tace ita matar aure ce.