Rahotanni sun bayyana cewa, duk da tallafin da gwammatin tarayya ta bayar a fannin shigo da kayan abinci daga kasashen waje, farashin kayan abincin yayi tashin gwauron zabi.
Rahoton yace Farashin kayan abincin da ake shigowa dasu daga kasashen waje ya tashi da kaso 37.65 kamar yanda hukumar kididdiga ta kasa, NBS ta sanar.
An fitar da wadannan alkalumane a tsakanin watannin Disamba zuwa Najairu.
Hakanan rahoton yace duk bayan wata, farashin kayan abincin yana kara tashi da karuwa.