Tsohuwar ‘yar kwallon Najeriya, Iyabo Abade wadda yanzu Namiji ce da sunan James Johnson na neman taimakon Naira Miliyan 69.7 dan ta samu ta rika haihuwa.
Iyabo ta bugawa Najeriya was a tsakanin 1997 da 2000. Kuma a shekarar 2004 ne aka canja mata halitta a kasar Amurka ta koma Namiji.
Tsohon ministan babban birnin tarayya a wancan lokacin, Malam Nasiru El-Rufai ne ya dauki nauyin aikin da aka mata.
Saidai kamin kace wani abu, Ita dai Iyabo an haifeta ne a matsayin mata maza, watau tana da azzakari da farji irin na mata.
Dan hakane ta zabi daya ko kuma aka duba wanda yafi karkata aka gano Namiji ne kuma aka mata aiki ta koma cikakken Namiji.
Saidai tana bukatar a kara mata aiki dan ta samu ta rika haihuwa.