Friday, December 5
Shadow

A bayyana mana sunayen Maqiya Dimokradiyya da suka so yiwa Gwamnatin Tinubu juhyin Mulki>>Mahdi Shehu ya roki Gwamnatin Tarayya

Dan Gwagwarmaya, Mahdi Shehu ya bayyana cewa, ‘yan Najeriya suna nema kuma suna da ‘yancin a sanar dasu sunayen sojojin da suka shirya yiwa Gwamnatin Tinubu juyin Mulki.

Ya bayyana hakane a shafinsa na X inda yace sati uku kenan ana ta rade-radin cewa an yi yunkurin yiwa shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu juyin Mulki.

Yace magana dai tun ana jita-jita har ta zama gaskiya inda yace ya kamata a daina boye-boye a fito a gayawa ‘yan Najeriya su waye suka shirya wannan juyin Mulki?

Karanta Wannan  Kalli Bidiyon yanda wani ya kutsa kai tsakanin jami'an tsaro ya kama Nownuwwan shugabar kasar Mexico a wajan taro

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *