
Tsohon Ministan tsaro, T.Y Danjuma ya bayyana cewa, Gwamnati ita kadai ba zata iya baiwa mutane kariyar da ya kamata ba.
Yace dan kawo karshen matsalar tsaro da garkuwa da mutane dole sai mutane sun tashi tsaye sun kare kansu.
Ya bayyana hakane a wajan wani taro a karamar hukumar Takum ta jihar Taraba.
Yace a bayama ya taba fadar haka a Wukari, kuma gashi ya sake nanatawa.