
‘Yar Fafutuka, A’isha Yesufu ta bayyana cewa, a cikin hadakae ‘yan Adawa da aka yi zuwa jam’iyyar ADC, Peter Obi ne kadai zai iya cin zabe a shekarar 2027.
A’isha ta bayyana cewa, Jam’iyyu 3 ne ke da jama’ar da babu kamarsu a Najeriya, APC, PDP da kuma Peter Obi.
Tace amma APC da PDP duk sun rasa jama’arsu inda tace jama’ar peter Obi ne kadai suka rage.
Tace ya ragewa hadakar ‘yan Adawa su baiwa Peter Obi takara ko kuma jiki magayi.
A’isha Yesufu tace rashin baiwa Peter Obi takara zai sa mutane da yawa ba zasu fito yin zabe ba abinda zai sa Tinubu ya sake cin zabe kenan.