Gwamnatin shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ta bayyana cewa ta yi nasarar yin maganin kungiyar Boko Haram.
Gwamnatin ta bayyana hakane ta bakin sakataren gwamnatin tarayyar, George Akume.
Ya bayyana hakane a Abuja wajan kaddamar da wani Littafi da aka yi kan cika shekara daya da kafuwar Gwamnatin Tinubu.
Yace babu wanda zai yi jayayyar cewa gwamnatin Bola Ahmad Tinubu ta yi nasarar gamawa da Kungiyar Boko Haram.
Saidai yace har yanzu suna yaki da Kungiyar masu garkuwa da mutane.