
Rahotanni sun ce a karin farko an ga Sauro a kasar Iceland.
Kasar Iceland dai itace daya tilo da babu sauro a Cikin a tsakanin kasashen Duniya.
Dalili kuwa shine kasar na da tsananin sanyi wanda sauro baya iya rayuwa a ciki.
Sannan kuma basu da ruwa dake kwanciya sosai wanda shima hakan na taimakawa wajan tara sauro.
Saidai duk da haka gashi a karin farko a yanzu an ga sauro a kasar.