Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya sakawa dokar haramta yin luwadi, Madigo da daudu ko saka kayan mata, da yin zane a jiki wanda aka fi sani da Tattoo a gidan soja.
Hakanan kuma dokar ta haramtawa sojojin huda jikinsu, irin su hudar kunne ko hanci da sauransu, sannan ba’a yadda soja ya sha giya a bakin aiki ko kuma ko da baya bakin aiki.
Wannan na kunshene a cikin sabuwar dokar aikin soja da shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya sanyawa hannu a watan Disamba na shekarar 2024.
Hakanan sabuwar dokar ta haramtawa sojojin shiga kungiyar asiri ko kuma harkar siyasa.