Friday, February 7
Shadow

A karin farko, Shugaba Tinubu ya sakawa dokar haramtawa sojojin Najariya yin Luwadi, Madigo da shan giya

Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya sakawa dokar haramta yin luwadi, Madigo da daudu ko saka kayan mata, da yin zane a jiki wanda aka fi sani da Tattoo a gidan soja.

Hakanan kuma dokar ta haramtawa sojojin huda jikinsu, irin su hudar kunne ko hanci da sauransu, sannan ba’a yadda soja ya sha giya a bakin aiki ko kuma ko da baya bakin aiki.

Wannan na kunshene a cikin sabuwar dokar aikin soja da shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya sanyawa hannu a watan Disamba na shekarar 2024.

Hakanan sabuwar dokar ta haramtawa sojojin shiga kungiyar asiri ko kuma harkar siyasa.

Karanta Wannan  Atiku ya bukaci majalisa ta ƙara wa’adin mulkin Shugaban ƙasa zuwa shekara 6 sannan a mayar da mulkin Najeriya karba-karba tsakanin Kudu da Arewa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *