
Bayan da ‘yar jarida Dr. Sandra Duru ta yiwa Sanata Natasha Akpoti Tonon Silili, inda tace sun yi waya kuma ta nadi maganar da suka yi inda Sanata Natasha Akpoti ta mata tayin Miliyan Naira 200 dan ta kalawa Sanata Godswill Akpabio sharrin cewa yana safarar sassan jikin mutane, Sanata Natasha Akpoti ta karyatata.
Natasha tace bata ma san ‘yar Jaridar ba.
Saidai daga baya da aka dameta da tambaya, ta amsa cewa lambar wayar da ‘yar Jaridar ta nuna sun yi magana da ita, tatace.
Watau kalaman da ake zarginta da furtawa ta furtasu.
Ko da dai Sanata Natasha Akpoti ta nace akan cewa bata furta wadancan kalamai ba, to lallai bai kamata mutane su ci gaba da yadda da maganganunta ba.