Monday, September 21
Shadow

A mulkin Tinubunnan nima yunwa ta kamani>>Inji Rotimi Amaechi

Tsohon ministan sufuri, Rotimi Amaechi ya bayyana cewa, Yunwa ta kamashi.

Amaechi ya bayyana hakane a wajan taron zagayowar ranar haihuwarsa.

Yace Dukkan mu nan muma cikin yunwa, idan baku ciki ni ina cikin yunwa.

Amaechi yace duk da yana APC amma bai zabi Tinubu ba a matsayin shugaban kasa ba.

Amaechi dai shine yazo na 2 a zaben fidda gwani na jam’iyyar APC a shekarar 2022 wanda Shugaba Bola Ahmad Tinubu ya lashe zaben.

Yace idan suka dage a matsayinsu na ‘yan Adawa zasu iya kwace mulki daga hannun Tinubu.

Karanta Wannan  Ba zan shiga hadakar su Atiku ba saboda ba zasu yi nasara ba, Tinubu ne zai sake cin zabe a 2027>>Inji Tsoho Gwamnan Benue, Ortom

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *