Friday, July 17
Shadow

Ku kara Hakuri, an kusa shan jar miya>>Shugaba Tinubu

Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya bayyanawa ‘yan Najeriya cewa saukin rayuwa na nan kusa da bayyana.

Ya bayyana hakane ta bakin me magana da yawunsa, Bayo Onanuga inda yace kowane sako da lungu na kasarnan zai shaida alfanin tsare-tsaren gwamnatinsa wanda nan gaba kadan za’a fara gani.

Shugaba Tinubu yace a lokacin da ya hau mulki NNPCL baya iya kawo man fetur saboda bashi ya masa yawa yace amma a haka yayi kokari aka samu sauki.

Yace kuma ‘yan Najeriya da dama sun samu budin arziki a zamanin milkinsa.

Karanta Wannan  A Zaman Da Muka Yi Da Ku Babu Wata Yarjejeniya Dake Da Alaka Da Cewa Ba Za A Kara Farashin Man Fetur Ba, Martanin Gwamnatin Tarayya Ga Kungiyar Kwadago

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *