Friday, December 5
Shadow

A shekaru 2 da ka yi kana mulki, baka tsinana komai ba sai shegiyar karya kawai>>Kungiyar Kare muradun yarbawa ta Afenifere ta caccaki shugaba Tinubu

Kungiyar kare muradun Yarbawa ta Afenifere ta caccaki shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu da cewa a shekaru 2 da yayi yana mulki bai tsinana komai ba sai karyar nasarar da babu ita a zahiri.

Kungiyar ta bayyana hakanne ta bakin sakatarenta, Oba Oladipo Olaitan inda tace Alkawuran kawo sauyi da yawa ‘yan Najeriya sun juya sun zama bala’i.

Kungiyar tace masana’antu sun durkushe, Sai yawan ciwo bashi ga kuma matsanancin Talauci da ake fama dashi a mulkin na Tinubu.

Kungiyar ta kuma ce shugaba Tinubu baya bin tsarin doka inda ta zargeshi da son mayar da Najeriya a karkashin tsarin jam’iyya daya.

Kungiyar tace sakamakon shekaru biyu da Tinubu yayi akan Mulki sun nuna cewa, dukkan wani bangare a ci gaban rayuwa ya samu ci baya a Najeriya tun bayan da Tinubu ya zama shugaban kasa.

Karanta Wannan  Idan kabar mu siyasar ka ta zo karshe>>Jam'iyyar ADC ta gayawa Peter Obi

Kungiyar tace kuma abin takaici shine yanda Gwamnatin Tinubu taki daukar alhakin wannan gyara inda take dorawa ‘yan Najeriya laifi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *