Thursday, April 16
Shadow

A shekarar 2020, ya sayi kayan abinci na Naira dubu ashirin da biyar, a shekarar 2026 ya koma ya sake sayen irin wadannan kayan abincin komai da komai saidai farashinsu ya koma Naira dubu dari da arba’in da bakwai

Wannan wani dan Najeriya ne da a shekarar 2020 ya sayi kayan abinci akan Naira 25,000.

Saidai a shekarar 2026 da muke ciki ya koma ya sake sayan kalar wadannan kayan abincin komai da komai saidai farashinsu ya karu zuwa Naira 147,000.

Hakan na nufin farashin kayan ya karu da kusan kaso 6 kenan.

Ya kuma wallafa rasit din abin a shafinsa na X.

Lamarin dai ya dauki hankula sosai inda akai ta tattauna yanda farashin kayan masarufi ke kara tashi.

Karanta Wannan  Muna goyon bayan saukar Ganduje daga shugabancin jam'iyyar APC, ba rikici bane ya faru, muna tsaftace jam'iyyar mu ne dan gobe shiyasa Ganduje ya sauka>>Inji Gwamnonin APC

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *