Idan dai ba wani canji aka samu ba, A cikin wannan satin ne ake sa ran ‘yan kasuwa zasu fara daukar man fetur daga matatar mai ta Fatakwal.
Me yada labarai na kungiyar ‘yan kasuwar man fetur din ta PETROAN Joseph Obele ne ya bayyana haka a wata ganawa da yayi da jaridar Punchng.
Ya bayyana cewa, tun bayan da Matatar man ta dawo aiki a watan Nuwamba, gidajen mai na NNPCL ne kawai take baiwa man amma suma suna sayen manne daga gurin NNPCL wanda ake shigo dashi daga kasar waje.
Ya koka da cewa amma ana sayar musu mai da tsada a fatakwal fiye da yanda NNPC din ke sayar da man a Legas inda yayi kiran a rika sayar musu a farashi daya.