Saturday, March 15
Shadow

A wannan shekarar kowa zai ga amfanin gyare-gyaren da gwamnatina ta yi, za’a ji dadi>>Gwamnatin Tinubu

Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa, a wannan shekarar da muke ciki ne za’a fara shaida romon gyare-gyaren da Gwamnatin Shugaba Bola Ahmad Tinubu ta yi.

Wasu daga cikin gyare-gyaren da Gwamnatin ta yi sun hada da cire tallafin man fetur, kara kudin wutar lantarki, kara kudin kira dana data, wanda wadannan abubuwa sun jefa ‘yan Najeriya cikin matsi.

Saidai da yake magana kan lamarin, Ministan yada labarai, Muhammad Idris ya bayyana cewa a wannan shekarar da muke ciki za’a fara ganin amfanin wadannan gyare-gyaren.

Ya bayar da misali da kasafin kudin shekarar 2025 na Naira Tiriliyan 54.2 wanda yace tun da ake a kasarnan ba’a taba yin kamarsa ba.

Karanta Wannan  Sanata Ali Ndume yayi Allah wadai da kama Hamdiya Sidi saboda kokawa da ta yi da kisan da 'yan Bìndìgà suke yi a jihar Sokoto

Yace wannan kasafin kudi an tsarashine dan kawowa ‘yan Najeriya ci gaba da saukin rayuwa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *