Monday, March 24
Shadow

Babu wanda ya isa ya sauke Sanata Godswill Akpabio daga mukaminsa saboda wannan dan zargin da Natasha tai masa>>Inji Basaraken jihar Bayelsa

Basaraken jihar Bayelsa kuma shugaban sarakunan jihar, Bubaraye Dakolo Agada IV, ya bayyana cewa babu wanda ya isa ya sauke Kakakin majalisar dattijai, Sanata Godswill Akpabio.

Ya bayyana cewa saboda wannan dan zargin da sanata Natasha Akpoti ta yi masa, bai isa ya sa a saukeshi ba.

Yace su suna tare da Sanata Godswill Akpabio saboda dansu ne.

Yace ya kamata awa Sanata Akpabio adalci kuma a kafa kwamitin bincikw da zai binciki lamarin.

Yace Sanata Godswill Akpabio ya kawowa Najeriya ci gaba sosai.

Karanta Wannan  Babu shugaban kasar da yana cikin hankalinsa zai jawoka jikinsa saboda yanda ka yi Alfahari da aika Tsohon shugaban kasa, 'Yar'adua Kabari, Shehu Sani ya gayawa El-Rufai

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *