Friday, December 5
Shadow

A yau ne ake sa ran kasar Amurka zata fitar da bayanai na zargin shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu da safarar miyagun Kwàyòyì, Saidai fadar shugaban kasa da APC sun ce wannan ba wani abu bane, Duk abinda ya faru kamin Tinubu ya zama shugaban kasa ba’a sakashi a lissafi

A yau ne ake sa ran hukumomin kasar Amurka na FBI zasu saki bayanai akan zargin shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu da safarar miyagun kwayoyi a Birnin Chicago na kasar.

Ana zargin Tinubu da asu mutane 3 Lee Andrew Edwards, Mueez Akande, da Abiodun Agbele a shekarun 1990 sun yi safarar miyagun Kwayoyi wanda shari’ar take kan Gudana.

Lauyoyi da musamman ‘yan Adawar shugaban kasar na neman a saki bayanai game da wannan binciken dan a san wanene shugaban kasar.

A baya ba’a samu hadin kan hukumomin kasar Amurkar ba game da sakin bayanan, amma a yanzu sun amince kuma a yau, Juma’a ne ake sa ran sakin wadannan bayanan.

Karanta Wannan  Kalli Bidiyo: Yanda Gwamna Soludo ke Rawar murnar sake lashe zaben Gwamna

Saidai fadar shugaban kasa ta bakin me magana da yawun shugaban kasar, Bayo Onanuga tace tabbas lauyoyi na kan binciken wannan magana.

Saidai fadar tace bayanan ko da an sakesu ba zasu kawo wani sabon abu da ba’a sani ba.

Itama dai jam’iyyar APC tace bayanan dama can ba’a boye suke ba dan haka ko da an sakesu babu wani sabon abu da za’a sani wanda ba’a sani ba a baya.


Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *