Kungiyar kwadago ta NLC ta soki shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu kan Karin kudin man fetur din da aka yi inda ta zargeshi da yaudara.
Kungiyar tace Tinubu ya yaudaresu suka amince da Naira dubu 70 a matsayin mafi karancin Albashi bisa alkawarin ba za’a kara farashin man fetur ba amma ya yaudaresu.
Shugaban kungiyar, Joe Ajaero ya bayyana hakan a cikin sanarwar inda yace suna kiran a janye wannan kari ko su dauki mataki.
Yace zasu ci gaba da kasancewa tare da mutane a kowane irin hali.