Wednesday, January 15
Shadow

A yaune Ministan kudi zai gabatar wa da shugaba Tinubu sabon daftarin mafi karancin Albashi

Ministan kudi, Wale Edun a yau ne ake sa ran zai gabatarwa da shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu da sabon daftarin mafi karancin Albashi.

Ko da ita kanta kungiyar kwadago, NLC ta dage zaman ta da gwamnatin tarayya sai yau din Alhamis da ake tsammanin sake ganin nawane gwamnatin tarayyar zata kara akan Naira dubu 60 da a baya NLC din ta ki amincewa da ita a matsayin mafi karancin Albashi.

Saidai a rahotanni na baya, kungiyar TUC tace ba zata amince da Kari dan kadan ba akan Naira dubu 60 din.

Sannan kuma tace ba ta dage akan sai an biyata Naira Dubu 400 ba, kawai dai abinda take nema shine a biya albashi da zai wadaci ma’aikaci.

Karanta Wannan  Hotuna: Tsohon Shugaban Kasa Muhammadu Buhari Ya Karbi Bakuncin Tsohon Ministan Yada Labaransa, Alhaji Lai Mohammed A Gidansa Dake Daura, Jihar Katsina Yau Lahadi

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *