
Shugaban Hukumar OSC, shirin Gwamnatin tarayya dake kula da canjawa tubabbun ‘yan Bindiga ra’ayi da mayar dasu cikin mutane da koya musu sana’a da basu jari, Yusuf Ali ya kaiwa hukumar NOA ziyara a hedikwatar ta dake Abuja.
Ya kai ziyarar ne ranar 2 ga wata Mayu inda shugaban hukumar ta NOA Lanre Issa-Onilu ya karbeshi, sannan kuma ya bayyana damuwa game da rashin fahimtar wannan shiri da mutane ke yi da yada labaran karya game da shirin.
Saidai shima Lanre Issa-Onilu yace a baya yana da shakku akan wannan shiri da yi masa wani irin kallo amma yanzu ya fahimci abina shirin ya kunsa.
Ya bayyana cewa wanna shiri na da matukar muhimmanci ga zaman lafiyar Najeriya.
Ya bayyana cewa mafi yawanci tubabbun ‘yan Boko haram din ba wai ra’ayi ne ya sakasu cikin lamarin ba, yawanci tursasa su aka yi ta hanyar garkuwa dasu da sauransu.
Yace idan gwamnati bata shiga lamarin tubabbun ‘yan Bòkò Hàràm din ba zasu iya zama cikin matsalar komawa ruwa sannan za’a iya rika waresu daga cikin al’umma.
Ya kuma jinjinawa Sojoji da sauran jami’an tsaro bisa kokarin da suke na wannan shiri. Sannan yri kiran a kara wayarwa da mutane kai game da shirin.
Shima a nashi bangaren Ali ya bayyana rashin jin dadin yanda mutane ke nuna kyama ga wadanda suka tuban.
Ya bayyana muhimmancin amfani da bangaren da bana karfi ba wajan yakar ‘yn Bindiga.