Abubuwan dake kara ruwan jiki suna da yawa, a wannana rubutu zamu bayyana wasu daga cikinsu.
Shan Ruwa:
Shan ruwa ce babbar hanyar samarwa da jikin mutum ruwa, masana na asibitin The Mayo Clinic na kasar Amurka sun bayar da shawarar cewa, namiji kamata yayi ya rika shan ruwa a kalla Kofi 15.5 watau Kofi goma sha biyar da rabi a kullun.
A yayin da ita kuma mace kamata yayi ta rika shan Kofi 11.5 watau Kofi goma sha daya da rabi kullun Dan samun isashshen ruwa a jiki.
A shawarce ana son mutum ya rika shan ruwa a duk sanda ya ci abinci ko yaci wani Abu irin su masara, Gyada, kuli, cincin, cake da sauransu.
Ana kuma son mutum ya rika shan ruwa tun kamin ya ji kishirwa.
Hakanan mutum ya sha ruwa a yayin da yake aikin office, ko gudu ko tafiya me nisa ko motsa jiki, ko tukin mota.
Ana son mutum ya rika shan ruwa bayan goge bakinsa da bayan yayi kashi.
Hakanan ana son mutum ya yawaita shan kayan marmari dan samun ruwan jiki sosai.
Irin su kankana.
Karas.
Gurji.
Lemu da sauransu.
Mutum kuma ya rage yawan shan lemun kwalba da musamman giya dan wasunsu na zuke ruwan jikin mutum.