Rahotanni da ga jihar Jigawa na cewa a kalla mutane 100 sun rasa ransu biyo bayan fashewar tankar mai a garin Majia dake karamar hukumar Taura a jihar Jigawa.
An ruwaito cewa fashewar ta auku ne a daren jiya Talata da misalin ƙarfe 11 na dare.
Rahotanni na bayyana cewa akalla sama da mutum100 Kuma sun jikata sanadiyar fashewar tankar man, kamar yadda gidan Rediyon Sawaba FM Hadejia suka ruwaito.