A yayin da cikinki ya kai watanni 8, abinda ke cikinki ya kai tsawon 11 inches.
A daidai lokacinne wani gashi me laushi dake lullube da abinda ke cikinki zai fara zubewa.
Idan namiji ne, a wannan lokacinne marainansa zasu zazzago kasa.
A wannan watanne zaki rika jin gajiya, sannan zaki rika nishi da kyar.
Jijiyoyi zasu iya fitowa rado-rado musamman a kafarki.
Zaki iya samun nankarwa.
Zafin kirji ko zafin zuciya na iya ci gaba, hakanan zaki iya ci gaba da fama da wahala wajan yin kashi.
Fitsari zai iya zubowa yayin da kika zo yin atishawa ko kuma kike dariya.
Wadannan abubuwanne zaki yi fama dasu yayin da cikinki ya kai watanni 8.