Wednesday, January 15
Shadow

Alamomin cikin wata uku

Idan cikinki ya kai watanni 3 zai zama yana da tsawon 2–3 inches ko kuma a ce 6–7.5 cm.

Yatsun hannuwa dana kafa zasu warware.

Kasusuwan abin cikinki zasu fara yin karfi.

Fata da farata zasu fara fitowa.

Alamun jinsin abinda ke cikinki zasu fara bayyana.

Koda zata fara samar da fitsari.

Alamun sweat glands zasu bayyana.

Ido zai zama a kulle.

Duka alamun daukar ciki daga wata na 2 zaki ci gaba da ganinsu a wata na 3 kuma zasu ma iya kara tsanani.

Zaki ci gaba da fama da rashin lafiya da safe.

Nonuwanki zasu ci gaba da girma.

Kan nononki zai kara girma ya kuma kara baki.

Karanta Wannan  Kumburin kafa ga mai ciki

Nauyinki ba zai karu ba sosai a wata na 3.

Mafi yawancin barin ciki na farko-farko ana yinshine a wata na 3.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *