Aikin Koda a jikin dan Adam shine tace datti da ruwan da bai da kyau daga cikin jini, a yayin da ta daina aiki, datti zai taru a jikin mutum.
Abubuwan dake kawo cutar koda suna da yawa, amma akwai sauran ciwuka dake kawo cutar, kamar ciwon suga, hawan jini da sauran ciwuka dake dadewa a jikin dan adam.
Ciwon koda na saka lalacewar jijiyoyi, da Raguwar karfin kashi, da kuma saka rama.
Idan cutar ta yi muni, hantarka ta daina aiki kwata-kwata, saidai a koma inji ya rika wanke maka koda.
Ire-ire da kuma Abubuwan dake kawo cutar Koda.
Cutar Koda me tsanani:
Wannan itace cutar koda da hawan jini yake haddasawa wadda kuma itace aka fi fama da ita.
Takan dade a jikin mutum kuma za’a ga kullun lamarin kara munana yake.
Hawan jini ta haddasa turawa koda jini da yawa wanda hakan ke sa ta rika aiki fiye da yanda ya kamata wanda a karshe har ta tsaya.
Hakanan shima ciwon sugar yana taimakawa sosai wajan kamuwa da irin wannan cutar koda.
Akwai kuma Kidney stones: Wannan ma cutar koda ce wadda wasu abubuwa masu karfi ke taruwa, yawanci ana futsarar dasune. Sukan sa mutum ya ji zafin fitsarinsa sosai. Itama wannan cuta ana yawan fama da ita.
Akwai kuma Glomerulonephritis:
Wannan yakan sa Kodar mutum ta kumburane kuma ana samun hakan daga shan kwayoyi, kamin ko bayan haihuwa, ko kuma wata karamar cuta, yawanci kodar kan koma daidai da kanta.
Akwai kuma cutar koda da ake kira da Polycystic kidney disease:
Ita wannan cuta takan sa wani abu ya kumbura akan kodar mutum wadda a karshe yakan hana kodar aiki da kyau.
Amma mafi yawanci wannan kumburi bashiwa kodar Illa.
Akwai kuma Urinary tract infections:
Wannan cutar fitsari ce wadda ke da alaka da Koda. Amma idan aka yi maganinta da wuri babu wata illa.
Saidai idan aka barta, zata iya zama illa ta kai ga lalata Koda.
Abubuwan dake kawo ciwon koda:
Abubuwan dake kawo cutar Koda sun hada da:
- Ciwon Hawan jini.
- Ciwon Suga.
- Cutar yawa ko rashin fitsari da aka ki magamcewa
- Ana gadonta
- Tsufa na kawota
Amma yawanci ciwon hawan jini da ciwon suga ne ke kawo cutar Koda.
Alamomin Ciwon Koda:
Yawancin ciwon koda bai cika bayyana da wuri ba sai ya kai matakin da ya ta’azzara. Amma ga wasu alamomi na farko dake nuna cewa mutum na da koda:
- Gajiya
- Kasa nutsuwa
- Kasa Bacci
- Rashin sha’awar cin abinci
- Wani sashe na jikinka ya rika motsi haka kawai.
- Kumburar kafa da gwiwa
- Kumburar idanu da safe
- Bushewar fata
- Yawan fitsari musamman da dare.
Idan kuma cutar ta yi tsanani sosai, ana ganin alamomi kamar:
- Tashin zuciya
- Amai
- Rashin jin sha’awar Jima’i
- Da canjin Fitsari.
Abincin mai ciwon koda:
Abinci mai gina jiki na da matukar muhimmaci wajan magance ciwon koda, kusan daya yake da shan magani, abincin mai ciwon koda kamar yanda masana suka bayyana shine:
- Kifi
- ‘Ya’yan itatuwa, lemu, ayaba, abarba, da sauransu.
- Ganye irin su alayyahu, kabeji, zogale da sauransu.
- Gero, Alkalama, Dawa, Masara, da sauran hatsi.
- Idan ana ahan giya a daina.
- Idan ana shan taba a daina.
- A rage shan gishiri.
- A eika motsa jiki akai-akai
Rigakafin Ciwon Koda:
- A rika shan ruwa akai-akai.
- Idan kana da ciwon suga karka bari jininka ya hau.
- Rage shan gishiri.
- A daina shan giya.
- A daina shan taba.
- A daina shan magani ba tare da umarnin likita ba dan kuwa wasu magungunan na lalata koda.
- A rage yan cin jan nama da kaji.
Ana warkewa daga ciwon koda?
A’a. Amsar kenan, musamman ga cutar koda me tsanani, ba’a warkewa daga ita, saidai akwai magunguna da hanyoyi da ake bi wajan rage radadinta musamman idan bata kai matakin kisa ba.
Shin me ciwon koda yana dadewa kamin ya mutu?
Me ciwon kodar da bai samu kulawa ba, tana kisa farat daya. Cikin kwanaki kadan mutum na iya mutuwa. Amma idan aka samu kulawa me kyau, masana sun ce ana iya rayuwa har tsawon shekaru 10 ko sama da haka.
Ciwon koda nahana haihuwa?
Me ciwon koda, mace ko namiji na iya haihuwa. Saidai idan cutar ta yi tsanani sosai tana hana haihuwa.
Zuma na maganin koda?
Zuma na maganin ciwon koda wanda ake kira da kidney stones wanda muka yi jawabi a sama, dunkulen abubuwane da suka hade waje daya sune ake kira Kidney Stones.
Yanda ake amfani da zuma shine, ana hadata da lemun tsamine, cikin gaggawa suke tarwatsa Kidney stones kuma a warke, saidai bamu samo cewa ko zuma na maganin cutar koda me tsanani ba.
Hakanan Zuma na taimakawa Koda yin aiki sosai yanda ya kamata.
Maganin ciwon koda na gargajiya
Ya danganta da irin ciwon kodar da ake fama dashi, idan sai Kidney stones ne, to za’a iya amfani da zuma kamar yanda muka bayyana a sama.
Wadannan bayanai ingantattu ne daga masana kiwon lafiya.Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:
A shafin twitter zaku same mu a @hutudole
A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa
Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole