Wednesday, January 15
Shadow

Alamomin namiji mazinaci

Namiji Mazinaci ba’a ganeshi a fuska amma akwai alamun da zai nuna miki wanda zaki san cewa lallai ba soyayyar gaskiya ce yake miki ba.

Wadannan Alamomi sun hada da:

Zai rika son ya taba jikinki a koda yaushe.

Zai rika son ya rika miki maganar batsa a ko da yaushe.

Zai nemi yayi zina dake.

Idan zai baki abu, ba zai baki haka siddan ba sai ya nemi yin lalata dake.

Zai rika nuna miki hotuna da Bidiyon batsa.

Ba zai damu da damuwarki ba, kawai dai abinda ke gabanshi shine ya kwanta dake.

Zai gindaya miki sharadin idan zai baki yadda yayi zina dake ba zaku rabu.

Karanta Wannan  Maganin dadewa ana jima i na bature

Zai miki alkawuran abubuwan ban mamaki idan kika yadda ya yi zina dake.

A mafi yawan lokuta idan Namiji ya nuna irin wannan halayya to zaki iya gane cewa mazinaci ne ba sonki yake tsakani da Allah ba.

Dan haka sai ki kiyayeshi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *