
Hukumar kula da albashin ma’aikata, RMAFC ta bayyana cewa tana shirin karawa ‘yan siyasa albashi inda tace Albashin nasu yayi kadan musamman lura da irin hidimar da ‘yan siyasar kewa Al’umma.
Shugaban hukumar, Mohammed Shehu ne ya bayyana hakan a yayin wani jawabi A Abuja ranar Litinin inda yace a yanzu haka albashin shugaban kasa Naira Miliyan 1.5 ne sannan albashin Ministoci kasa da Naira Miliyan 1 ne kuma tun shakerar 2008 ba’a musu karin Albashin ba.
Yace abin mamaki ne ga mutane da yawa ace wai shugaban kasar Najeriya me mutane Miliyan 200 ace ana biyansa Albashin Naira Miliyan 1.5 a wata.
Yace ba zai yiyu ace Minista ana bashi Albashin Kasa da Naira Miliyan 1 ba sannan ace ba zai yi sata ba, yace ba zai yiyu ace ana biyan Gwamnan CBN da sauran manyan jami’an gwamnati albashi ninkin na shugaban kasa ba.
Saidai Kungiyar Kwadago ta yi watsi da wannan yunkurin inda tace albashin kawai ake fada amma akwai lawus da yawa da ake biyan shugaban kasar.