
Rahotanni daga kasar Morocco sun bayyana cewa, kasar Algeria ta fitar da Dr. Congo daga gasar AFCON bayan ta mata ci 1-0.
A yanzu Algeria zata buga wasan Quarter final da Najeriya.
Bayan wasan, an ga shahararren dan kasar Dr. Congo da ya rika tsayawa a tsaye duk wasansu yana daga hannu sama kamar Kungi yana share hawaye.
Mutumin me suna Patrice Lumumba ya kuma gana da shugaban CAF, Dr. Patrice Motsepe.