
A yayin da ake ta jin abubuwan da suka faru a rayuwar tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari daga bakin matarsa, A’isha Buhari da ‘ya’yanta mata, Dansa Namiji, Yusuf Buhari bai ce uffan ba.
Iyalan tsohon shugaban kasar sun rika bayyana abubuwan da ya faru a mulkinsa a cikin wani littafi da aka rubuta na tarihin Rayuwarsa.
Rahotanni sun ce, Tun yana raye, shugaba Buhari yace ba zai rubuta littafi akan tarihin Rayuwarsa ba. Wasu a ganin cewa dalili kenan da yasa Yusuf Buhari bai ce uffan ba kan rayuwar mahaifin nasa dan girmama abinda yake so.