
Bayan zaman kotun da aka yi dashi a Jihar Kaduna jiya, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai ya zanta da ‘yan Jarida.
Inda ya gayawa jaridar Daily Trust cewa, idan ya fito, sune na farko da zai yi hira dasu.
A jiya ne dai ICPC ta gurfanar da malam Nasiru Ahmad El-Rufai a kotu inda aka zargeshi da almundahanar kudade wanda ya karyata.