
Tauraruwar Tiktok da ta shahara wajan Karatun Qur’ani da fadakarwa, Malam Hafsah ta koka da yanda Gwamnan Kanox Abba Kabir Yusuf ya biya mata Umrah amma da sunayen wadanda zasu tafi suka fito, bata ga sunanta ba.
Ta yi Bidiyo a shafinta na Tiktok inda take kokawa da cewa ‘yan uwa da abokan arziki duk sun san da zuwanta kuma ana ta mata fatan Alheri amma gashi yanzu suna ya fito babu sunanta.