Tuesday, March 24
Shadow

Allah Sarki Kalli Bidiyon: Yanda kasar Nijar ta koro ‘yan Najeriya guda 708 da suka je Chirani

Yan Najeriya 708 ne da suka je Chirani kasar Nijar, kasar ta taso keyarsu ta dawo dasu gida Najeriya.

Hukumar bayar da agajin gaggawa ta kasa, (NEMA) ta karbi ‘yan Najeriyar bayan da aka dawo dasu gida ranar Litinin.

Shugaban Hukumar NEMA na Kano, Dr Nura Abdullahi ne ya tabbatarwa da manema labarai hakan bayan karbar ‘yan Najeriyar a filin jirgin sama na Malam Aminu Kano International Airport dake Kano.

An kawo su ne a manyan motocin 12 da misalin karfe 4:08 pm. Inda aka fara tantancesu.

Guda 292 mazane sai kuma guda 416 wanda matane da kananan yara.

Kuma yawanci sun fitone daga jihohin Katsina, Kano, Jigawa, Benue, Borno, Yobe, Zamfara, Kaduna, Kogi da Niger.

Karanta Wannan  A yau Juma'a aka daura auren Jarumi ABDUL M SHAREEF da Jaruma MARYAM MALIKA

Ya bayyana cewa an basu abubuwan bukata na gaggawa da suka hada da abinci, kulawar lafiya da gidajen sauro da sauransu inda yace ana shirin mayar dasu gidajensu.

A kafafen sada zumunta kuwa, tuni Bidiyon ya yadu kan yanda aka dawo da ‘yan Najeriyar daga kasar Nijar.

An ga daya daga cikinsu yana bayar da labarin irin cin mutuncin da aka musu.

Yace sai da ya je Nijar ne ya tabbatar cewa shuwagabannin Najeriya na kula damu kuma yasan muhimmancin zama a Najeriya.

@deopenlens

“We urge the Niger Republic to stop the mistreatment of Nigerians and ensure their safe and dignified departure, rather than subjecting them to humiliation.”#Nigerstophumiliation #abis_fulani #arewapeople #arewa__tiktok #hausatiktok @VDM 🦡 @Arewa_Latest_News @Freedom Radio Nigeria @bbchausa @ARMY LEGEND 🦅 @Abdourahamane Tchiani @United Voice Of Arewa @Voice_of_bazawara @Nigeria immigration service @Hon Bello elrufai @Ramadan17 @Sarkin mota @Ahmed XM @DJAB @Arewa Media

♬ original sound – De OpenLens 🇳🇬
@deopenlens

If we believe in One Africa, Why is Niger Republic Deporting Nigerians residing in Niger? #vdm #abis_fulani #nigeriatiktok🇳🇬🇳🇬🇳🇬 #danbello #armylegend @VDM 🦡 @Arewa_Latest_News @Freedom Radio Nigeria @ARMY LEGEND 🦅 @😘 joygiver 💆🧑‍⚕️🩺💕🇳🇬? @sasosadiq

♬ I Am Africa – Ancient Mother

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *