
Wannan malamin ya fito ya sassauta lafazi akan wa’azi me kaushi da yayi a baya akan rasuwar dan daba, Habu Dan Damisa na Kaduna.
Malam a yanzu yace, a dauna munana zato akan dan Damisa inda yace lamarinsa na ga Allah, in yaso ya azabtar dashi in yaso ya yafe masa.
Saidai da yawa sun ce malamin tsoro yaji kada yaran dan Damisa su illatashi ko kumama aikashi kiyama.
A baya dai malam yayi Allah wadai da irin rayuwar dan Damisa inda ya kushe harkar daba duk da dai wa’azi ne yayi.
Akwai wani matashi da ya fito yayi zagezage akan malamai, sannan ko a kasan Bidiyon malam an ga yanda ake mayar masa raddi masu zafi.