
Yunusa Ahmadu Yusuf kenan wanda aka fi sani da Buhun Barkono wanda ya rasu a dakin Otal bayan ya shiga shi da wata me suna Ruth.
Lamarin ya farune a ranar 8 ga watan Satumba inda bayan sun shiga dakin Yunusa Bai cin abinci saidai yayi ta kwankwadar giya, Kamar yanda rahotonni suka tabbatar.
Ruth ta samowa Yunusa maganin kara karfin kuzari wanda bayan da ya sha ne ya suma daga nan kuma sai ya rasu.
Tuni aka tafi dashi asibiti dan biciken abinda ya kasheshi.
Lamarin ya farune a Karu-Jikwoyi, Abuja.