
Sojan Najeriya da aka kora daga aiki saboda yace ‘yan siyasa su saka ‘ya’yansu aikin soja ya fito a karin farko yayi magana.
Sojan yace an kamashi ne a bakin aiki inda yake a Maiduguri na tsawon shekaru 4 da watanni 9.
Yace an kaishi aka kulle sau biyu kawai ake bashi abinci.
Yace ya sha wuya amma daga baya aka koreshi daga aiki.
Yace a Najeriya yanzu ba dama mutum ya fadi gaskiya.