Friday, December 5
Shadow

‘Allah Ya isa duk wanda ya ce APC nake yi wa aiki’ – Inji Shugaban PDP Damagum

Shugaban babbar jam’iyyar hamayya a Najeriya, PDP, Ambasada Umar Iliya Damagun, ya musanta zargin da wasu ke yi masa cewa yana yi wa jam’iyya mai mulkin kasar, APC aiki ne shi ya sa rikicin PDP din ya ki ci ya ki cinyewa.

A hirarsa da BBC Ambasada Damagun ya ce shi kam tsakaninsa da masu zargin cewa shi dan-amshin-shata ne na jam’iyyar APC, baa bin da za ice sai, ”Allah Ya isa.”

Ya ce : ”Allah ya isa tsakanina da duk wanda ya yi min wannan Kazafi, kuma Allah Zai yi mana shari’a in da zan shiga jam’iyyar APC da tun lokacin Buhari da na shiga.

”Kuma ina da tarihi tun da na shiga jam’iyyar PDP a 1999 ban taba sauya sheka ba. Dole wanda ba ya so na zai nemi yanda zai yaba min zargi don ya samu biyan bukatarsa. Na ce ma na je na yi mitin da Tinubu, a Ingila, wannan duk masu yin wannan na bar su da Allah.” In ji shugaban.

Karanta Wannan  Kalli Bidiyo: Wasu daga cikin Musulmai na cin kazantacciyar Halitta, Alade, da shan Giyya da Mu'amala da mata masu zaman kansu>>Inji Alpha Charles Borno

Dangane da zargin da wasu ke yi wa shugaban na PDP na kusanci da kuma alaka da Ministan Abuja kuma tsohon gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike, inda suke cewa wannan na daga cikin rashin iya shugabancinsa da kuma yi wa PDP zagon-kasa, Damagun ya mayar da martani da cewa:

‘Duk masu zargin yau ina alaka da Ministan Abuja, kan na san shi ko na yi alaka da shi da yawansu sun yi alaka da shi. Ni dai laifina guda daya a nan shi ne ban yardar musu yadda suke so su yi da shi su yi da shi ba.”

Game da yadda jam’iyyar ta PDP ta rasa wasu manyan kusoshinta da suka sauya sheka zuwa jam’iyyar APC mai mulki, shugaban nata ya ce hakan bai yi musu dadi ba

Karanta Wannan  Masanin Taurari yace a iya duban da suka yi basu ga cewa wata kasa zata kawowa Najeriya Khari ba a wannan shekarar

Alhaji Damagun ya ce jamiyyar tasu ta PDP na jin takaicin ficewar, duk da cewa wadanda suka fice din ba laifi aka yi musu ba, amma tana kokarin dinke barakar da ta kunno kai a cikinta har wasu ke ta fita.

”Dole mu ji takaici ko ba komai duk lokacin da ka rasa mutum ba ka jin dadi ko da mutum daya ne kana jimami.

”Amma kuma kamar yadda kullum nake fada babu inda kake gani an yi tirken mutane an sa musu tirke ka ce musu dole su tsaya inda suke.

”Yawanci al’amari yana tasowa idan mutum abubuwa suka faru zai nemi dalili da zai ce shi ya tafi.” In ji shi.

Sai dai kuma shugaban na PDP, ya kara da cewa yana alfahari da cewa duk wadanda suka sauya sheka, ba wanda zai iya fitowa ya ce jam’iyyar ta yi masa wani laifi:

Karanta Wannan  Kalli Bidiyon: Yanzu ace duk Sokoto ba gidan haya me Arha sai sama da Naira Miliyan 1, ta yaya samari zasu yi aure?

”Sai dai ma ta yi musu riga ta yi musu wando.”

Damagum ya ce, jam’iyyar ba ta da wata matsala wadda za a ce yau ta sa an yi bangarori a cikinta, ”PDP daya take.”

Ya ce gaskiya ne suna da matsaloli na cikin gida, domin jam’iyya ba ta taba rasa matsala ba saboda mutane ne shugabanninta, kuma mutane ne suke cikinta, sannan kowa yana da bukatunsa.

A kan haka ya ce dole a samu sabani, a kuma sa mu son-rai, ta yadda wani idan ba a yi masa yadda yake so ba, ”to kai ba ka iya ba.” Ya ce.

Shugaban ya ce, su suna yin jagorancin jam’iyyar ne bisa ka’idoji, sannan sun ki ba da kai ga masu son-rai shi ya sa dole a zarge su.

Ya ce, ”duk lokacin da aka ce ka zo shugabanci bayan an fadi zabe to akwai korafe-korafe ba iyaka.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *